Gwamnatin Jihar Adamawa ta Bukaci Jama’a Su Fito Tarbar Shugaba ƙasar Tinubu.

Gwamnatin Jihar Adamawa ta Bukaci Jama’a Su Fito Tarbar Shugaba ƙasar Tinubu.

Gwamnatin Adamawa ta sanar da rufe wasu manyan hanyoyi na wucin-gadi tare da bukatar jama’a su fito tarbar Bola Ahmed Tinubu yayin ziyarar aiki ta yini guda da zai kai jihar.

Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta ce an dauki matakin ne domin sauƙaƙa zirga-zirga da tabbatar da tsaro a lokacin ziyarar Shugaban Ƙasa, musamman a Yola da kewaye.

Hanyoyin da rufewar ta shafa sun hada da hanyar Filin Jirgin Sama zuwa Kofare ta Galadima Aminu Way/Bank Road, Jimeta Grade Interchange/Police Roundabout, Justice Buba Ardo Way, da wasu muhimman hanyoyi. Gwamnatin ta shawarci direbobi da su bi madadin hanyoyi a lokacin.

A cewar rahoton, Shugaba Tinubu zai kaddamar da manyan ayyukan raya kasa a jihar, ciki har da:

Sabon underpass a tsohon zagayen Bekaji

Faɗaɗa Bank Road a Yola

Makarantar zamani a Yola North

Kafa harsashin sansanin NYSC na dindindin a Malkohi

Ginin Kotun Babbar Jiha na zamani

Sabon ginin ofishin Gwamna da kuma ƙofar lantarki a Gidan Gwamnati.

Haka kuma, ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun kara tsaurara matakan tsaro a fadin jihar domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyi.

Gwamnatin jihar ta bukaci jama’a da su fito cikin lumana domin tarbar Shugaban Ƙasa tare da bin dukkan umarnin jami’an tsaro.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form