Sarkin musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, shugaban Hukumar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya yi kira ga Musulmai a fadin Najeriya da su fara nema sabon watan Ramadan nan da ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, wanda ya yi daidai da 29 Sha’aban 1447 A.H.
A wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi wacce sakataren NSCIA, Far. Is-haq Oloyede, ya sanya hannu, Sarkin ya jaddada muhimmancin ganin sabon watan don tantance farkon watan azumi da ibada, da tunani na ruhaniya ga Musulmai a duniya baki daya.
Wannan kiran na daga cikin al’adar Musulunci, inda bayyanar sabon watan Ramadan ke nuna karshen Sha’aban da fara Ramadan, wanda Musulmai ke gudunar da ibadan azumi daga wayewar gari zuwa faduwar rana, tare da ƙaruwar ibada da sadaka.
Tags
Labarai
