Daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a hedkwatar hukumar EFCC da ke Abuja, inda suka bukaci hukumar ta gaggauta bincike tare da gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bisa zargin almundahanar kudade.
Masu zanga-zangar, da ke karkashin wata kungiya mai suna Mega National Movement for Good Governance, sun rika rike alluna masu dauke da sakonni irin su “El-Rufai Ba Ya Sama da Doka” da “Ka Amsa Tuhume-tuhume, El-Rufai”.
Sun bayyana cewa zargin ya shafi badakalar kudi da ake zargin ya kai kusan Naira biliyan 432 a lokacin mulkinsa.
Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun yi yunkurin shiga harabar EFCC, amma jami’an tsaro suka hana su, duk da haka sun mika koke da bukatunsu ga hukumar.
Kakakin masu zanga-zangar ya ce manufarsu ita ce tabbatar da adalci, gaskiya da bin doka, ba siyasa ko tsangwama ba.
A martaninta, EFCC ta bayyana cewa tana mutunta ‘yancin jama’a na gudanar da zanga-zanga cikin lumana, tare da tabbatar da cewa za a bi ka’idojin doka wajen duba dukkan korafe-korafen da aka gabatar.
Ta ce za a tura bukatar zuwa sassan da suka dace domin daukar mataki.
Tags
Labarai
