Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, Ya rushe majalisar zartarwar jihar, tare da nada sabon sakataren gwamnati.

Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, Ya rushe majalisar zartarwar jihar, tare da nada sabon sakataren gwamnati.

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya rushe Majalisar Zartarwa ta Jihar tare da sallamar dukkan Mashawartansa na Musamman.

An sanar da hakan ne a cikin Sanarwar Gwamnati ta Musamman da aka fitar a birnin Port Harcourt ranar Alhamis, 12 ga Fabrairu. 
A cikin wannan sanarwa, gwamnan ya nada Onwuka Nzeshi a matsayin sabon Sakataren Gwamnati na musamman, inda ya maye gurbin Nelson Chukwudi, wanda aka sallama daga mukaminsa. Sai dai ba a bayyana dalilin sallamar Chukwudi ba.

Haka zalika Gwamna Fubara ya umarci dukkan kwamishinoni da mashawartansa na musamman da su mika ayyukansu nan take ga Sakataren Dindindin ko manyan jami’an da suka fi kowa girma a ma’aikatunsu.

Sanarwar ta kara da cewa:

> “Mai Girma Gwamna, Sir Siminalayi Fubara, GSSRS, Gwamnan Jihar Rivers, ya rushe Majalisar Zartarwa ta Jihar.
Mai Girma Gwamna ya umarci dukkan Kwamishinoni da Mashawartansa na Musamman da su mika ayyukansu ga Sakataren Dindindin ko manyan jami’an ma’aikata nan take.
Haka kuma, Mai Girma Gwamna ya nuna godiya mai zurfi ga wadanda suka bar Majalisar Zartarwa, tare da yi masu fatan alheri a rayuwarsu ta gaba.”

Bayan rushewar majalisar, ana sa ran Gwamna Fubara zai mika sabon jerin sunayen ‘yan takarar kwamishinoni ga Majalisar Dokoki ta Jihar Rivers, karkashin jagorancin Martin Amaewhule, domin tantancewa da tabbatarwa.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form