Ana cikin jimami a jihar Bauchi bayan rasuwar wani matashi, mai suna Kamal, wanda Allah ya yi ma rasuwa bayan ya kashe sama da Naira Miliyan 2 (₦2,000,000) wajen gyara masallacin da yake sallah, domin tarban watan Ramadan mai zuwa.
Kamal, wanda aka bayyana a matsayin matashi mai kwazo da imani, ya sadaukar da dukiyarsa wajen gyaran masallacin ne domin neman yardar Allah da lada a Lahira. Sai dai Abin takaici, bai samu daman ganin watan Ramadan din ba.
Iyali da al’umma sun bayyana jin dadin cewa aikin alherin da ya yi—na kudi naira N2,000,000 da ya kashe a masallaci—zai ci gaba da zama lada a Lahira.
Ana mika sakon ta’aziyya ga mutanen Magama Gumau, Jihar Bauchi, da dukkan al’ummar Musulmi.
Allah Ya gafarta wa Kamal, Ya sanya masallacin da ya gyara ya zama haske a kabarinsa, Ya kuma sa mu cika da imani idan lokacinmu ya yi.
Tags
Labarai
