'Yar Najeriya ta kafa tarihi a lokacin bude gasar Olympics na hunturu a ƙasar Italiya.

'Yar Najeriya ta kafa tarihi a lokacin bude gasar Olympics na hunturu a ƙasar Italiya.

A lokacin Bude Gasar Olympics ta Hunturu Milano Cortina 2026, marubuciya 'yar Najeriya, Maryam Bukar Hassan, wacce aka fi sani da Alhanislam, ta kafa tarihi inda ta zama ta farko daga Najeriya da ta ɗauki tutar Olympic a tarihin gasar ta duniya.

Yayin da ‘yan wasa ke yin tafiya a bayan tutocin kasashensu, tutar Olympic mai alamomin zobe biyar tana kasancewa ga mutanen da tasirinsu ya wuce gasar wasanni, wadanda tasirinsu ya shafi duniya baki daya da gina alaka tsakanin al’adu da jajircewa wajen fafutukar alheri da canji mai kyau.

A cikin bikin da aka kalla a ko’ina a duniya, wannan girmamawa ta samu Maryam, inda aka yaba mata a matsayin jakadiyar al’adu da fafutukar kawo canji mai kyau a cikin al’umma.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form