El-Rufai Zai Bayyana a Gaban EFCC Ranar Litinin Bayan Yunƙurin Kama Shi a Filin Jirgin Sama

El-Rufai Zai Bayyana a Gaban EFCC Ranar Litinin Bayan Yunƙurin Kama Shi a Filin Jirgin Sama

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, zai bayyana a gaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da ƙarfe 10:00 na safe ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026, a cewar lauyansa.

Lauyan El-Rufai, Ubong Esop Akpan, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan zargin yunƙurin da jami’an tsaro suka yi na kama tsohon gwamnan a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja, a yau Alhamis.

A cewarsa, jami’an tsaro sun tunkari El-Rufai ne jim kaɗan bayan isowarsa Abuja daga birnin Cairo na ƙasar Masar, ta jirgin Egypt Air mai lamba MS 877. 
Ya bayyana lamarin a matsayin take haƙƙoƙin kundin tsarin mulki da kuma cin zarafin doka.

Akpan ya ce gayyatar EFCC an kai ta gidan El-Rufai ne a lokacin da yake ƙasashen waje, wanda hakan ya sa neman gaggawar halartarsa ya zama abin da bai dace ba kuma mara ma’ana.

“An kai gayyatar EFCC gidan Malam El-Rufai ne alhali yana wajen ƙasar, don haka ba zai yiwu a nemi ya halarta nan take ba,” in ji Akpan.

Ya ƙara da cewa tun daga watan Disamba 2025, lauyoyin El-Rufai suka sanar da EFCC cewa zai amsa gayyatar da zarar ya dawo Najeriya.

“Jiya mun sanar da EFCC a sarari cewa zai zo ofishinsu da kansa da ƙarfe 10:00 na safe ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026,” in ji shi. “Yunƙurin kama shi duk da wannan tabbaci alama ce ta rashin bin ƙa’ida da tauye tsarin shari’a.”

Lauyan ya jaddada cewa babu wata hujja ta doka da za ta tabbatar da yunƙurin kama El-Rufai, yana mai cewa hakan ya saɓa da tanade-tanaden kundin tsarin mulki da ke kare ’yancin dan Adam.

Ya kuma bayyana cewa El-Rufai ya dawo Najeriya ne bayan jinya da hutawa a ƙasashen waje, duk da samun bayanai kan yiwuwar kama shi, kuma ya riga ya bayyana a bainar jama’a cewa a shirye yake ya fuskanci duk wata sahihiyar bincike.

Akpan ya bayyana abin da ya faru a filin jirgin sama a matsayin shiri tun tuni da aka yi, tare da kiran shi cin zarafin ikon gwamnati.

Lauyoyin El-Rufai sun buƙaci a dakatar da duk wani yunƙuri na kama shi ba bisa doka ba, a mayar masa da fasfot ɗinsa nan take, tare da neman afuwar hukuma kan abin da suka kira take mutuncinsa da haƙƙoƙinsa na asali.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form