Arsenal ta rasa damar ƙara faɗaɗa jagorancinta a saman teburin Gasar Firimiya ta Ingila bayan da ta tashi kunnen doki 1-1 da Brentford, lamarin da ya rage banbancin maki tsakaninta da Manchester City zuwa maki huɗu kacal.
Ƙungiyar Mikel Arteta ta samu nasara a minti na 60 lokacin da Noni Madueke ya zura ƙwallo da kai cikin raga bayan kyakkyawan tsalle. Sai dai Brentford ta dawo kan hanya bayan mintuna 10 kacal, inda Keane Lewis-Potter ya ci ƙwallon ramawa bayan jefa dogon kwallo da Michael Kayode ya yi.
Bayan samun ƙwallon kunnen doki, Brentford — wadda ta san cewa nasara za ta ɗaga ta sama da Liverpool a teburin gasar — ta nuna ƙwazo wajen neman ƙwallon nasara. Igor Thiago ya yi asarar babbar dama a lokacin ƙarin lokaci, abin da ya hana su samun cikakkiyar nasara.
A ɗaya bangaren kuma, Arsenal ma ta kusa cin ƙwallon nasara a mintunan ƙarshe bayan shigowar Gabriel Martinelli daga benci, sai dai golan ragar Brentford, Caoimhín Kelleher, ya hana shi zura ƙwallo a raga a cikin yanayi mai cike da ruɗani.
Sakamakon wasan ya bai wa Manchester City damar rage tazara a fafutukar neman kambun gasar. Kwanaki huɗu kacal da suka gabata a Anfield, ƙungiyar Pep Guardiola ta kusa faɗuwa baya da maki tara, amma yanzu ta koma cikin matsayi mai barazana ga Arsenal.
Arsenal, wadda ta ƙare gasar a matsayi na biyu a kakanni uku da suka gabata, har yanzu za ta kai ziyara zuwa filin Etihad a watan Afrilu, yayin da take ƙoƙarin kawo ƙarshen jiran shekaru 22 ba tare da lashe kofin Firimiya ba.
Tags
Labaran Wasanni
