Kungiyar kwallon kafar Barcelona ta sha Kashi a hannun Athletico Madrid da ci 4-0 a wasan kusa da na karshe na cin kofin gasar Copa del Rey.
Atletico Madrid ta nuna bajinta yayin da ta doke jagoran La Liga, Barcelona, da ci 4-0 a wasan farko na wasan kusa da na karshe na cin kofin gasar Copa del Rey a filin wasa na Metropolitano dake birni Madrid, yau Alhamis.
Barcelona, wacce ta lashe kofin a bara bayan ta doke Real Madrid da ci 3-2, ta sha mamaki yayin da Atletico ta mamaye wasan daga farko har ƙarshe.
Za a buga zagaye na biyu na wasan a filin Nou Camp na Barcelona a ranar 4 ga Maris, inda Barcelona za ta fuskanci babban kalubale wajen dakile bambancin kwallaye hudu da Atletico Madrid ta zura mata.
Tags
Labaran Wasanni
