Dalilin koma wa na Jam'iyyar APC – Gwamnan Kano

Dalilin da ya sa na koma APC – Gwamnan Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana dalilan da suka sa ya koma jam’iyyar APC, yana mai cewa matakin da ya dauka ya ta’allaka ne da muradin al’ummar Kano da ci gaban jihar gaba ɗaya.

Gwamnan ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne domin Jihar Kano ta samu damar yin aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayya, ta yadda hakan zai taimaka wajen jawo ayyukan raya kasa da tallafin gwamnati daga cibiyar mulki.

A cewarsa, ba batun siyasa ko bukatar kashi ba ne ya sanya ya sauya sheka, sai dai kokarin tabbatar da cewa al’ummar Kano sun amfana da manufofi da shirye-shiryen ci gaba da ake aiwatarwa a matakin kasa.

Ya kara da cewa komawarsa APC zai bai wa Kano damar shiga cikin cikakken tsarin aiwatar da manufar “Renewed Hope Agenda” ta Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, wadda ta mayar da hankali kan gyaran tattalin arziki da bunkasa ababen more rayuwa da inganta rayuwar ‘yan kasa.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa Kano jiha ce mai muhimmanci a siyasar Najeriya, don haka bai dace ta kasance cikin keɓantuwar siyasa ba. A ganinsa, hadin kai da zaman lafiya a fagen siyasa ne zai tabbatar da dorewar cigaba.

Tun da farko, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kasance mamba a jam’iyyar NNPP, amma ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar tare da dawowa APC, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce da kuma martani mabambanta daga bangarori daban-daban na siyasa a jihar Kano.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form