Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da biyan albashin watan Fabrairu da fansho tun da wuri ga ma’aikatan gwamnati da tsofaffin ma’aikata, domin sauƙaƙa musu shirye-shiryen shiga watan Ramadan.
Umarnin ya bukaci Babban Akanta na Jihar da ya gaggauta sakin kudaden domin ma’aikata da masu karɓar fansho su samu damar tanadin bukatun Ramadan cikin kwanciyar hankali.
Sanarwar ta fito ne ta bakin Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu, Mahmud Dantawasa, wanda ya ce matakin na nuna damuwar gwamnatin jihar ga jin daɗin ma’aikata da tsofaffin ma’aikata.
Gwamna Lawal ya kuma yi kira ga al’umma, musamman Musulmi, da su yi addu’o’i don zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jihar, tare da yi wa Musulmi fatan alheri a watan Ramadan mai albarka.
Tags
Labarai
