Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa zai kasance cikin tattaunawar nukiliya tsakanin Amurka da Iran a yau Talata kai tsaye daga birnin Washington, yayin da wasu jami’an Amurka ke birnin Geneva na ƙasar Switzerland.
Trump ya ce yana ganin Iran tana so a cimma yarjejeniyar, amma ya yi gargaɗi sosai cewa Iran za ta fuskanci mummunan sakamako idan ba ta kulla yarjejeniya ba.
Hakan na zuwa ne yayin da Amurka ta karfafa matsayinta a Gabas ta Tsakiya, ta hanyar tura manyan jiragen ruwanta masu dakon jiragen yaki, ya yin da Iran kuma ta gudanar da atisayen soji a gabar mashigar Hormuz, alamar cewa tana shirye ta mayar da duk wani martani idan aka farmake ta.
Tattaunawar tana karkashin tsari wacce ba kai tsaye ba tsakanin shugabannin biyu ba, amma ana sa ran zai zama wani muhimmin ɓangare na matsayin Amurka, tare da neman dakile shirye‑shiryen nukiliyar Iran da rage ƙarfinta.
Tags
Labarai
