Babban jami’in tsaron Iran ya kai ziyara Oman bayan tattaunawar nukiliya da Amurka.

Babban jami’in tsaron Iran ya kai ziyara Oman bayan tattaunawar nukiliya da Amurka.

Babban jami’in tsaron Iran ya kai ziyara Oman bayan tattaunawar nukiliya da Amurka.

Ali Larijani, sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Ƙoli a Iran, ya isa ƙasar Oman biyo bayan tattaunawar da aka gudanar a can tsakanin Iran da Amurka kan shirin nukiliyar Iran, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati a Iran suka ruwaito.

Larijani, wanda ke ɗaya daga cikin manyan mashawartan Jagoran Ƙoli na ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ana sa ran zai gana da Ministan Harkokin Wajen Oman, Badr al-Busaidi — babban mai shiga tsakani a tattaunawar — da kuma Sarkin Oman, Sultan Haitham bin Tariq Al Said. 
Hakan ya fito ne daga rahoton kamfanin dillancin labarai na gwamnati, IRNA, a yau Talata.

IRNA ta bayyana cewa “tattaunawa kan sabbin abubuwan da ke faruwa a yankin da kuma a matakin ƙasa da ƙasa” na daga cikin ajandar ziyarar Larijani birnin na Muscat, tare da “hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwar ɓangarorin Iran da Oman”.

Wasu masu sharhi na kallon wannan ziyara — bayan tattaunawar da aka yi kwanan nan a Oman — “a matsayin alama mai kyau da ke nuna wani mataki na ci gaba” a ƙoƙarin haɓaka tattaunawar.

Oman ta karɓi baƙuncin tattaunawar shirin nukiliyar Iran a makon jiya, da nufin kauce wa rikici tsakanin Iran da Amurka, a daidai lokacin da tashin hankali ke ƙaruwa da kuma yadda Amurka ke ƙara ƙarfafa rundunonin sojinta a yankin Gabas ta tsakiya.

Tattaunawar ta kasance sakamakon haɗaɗɗun ƙoƙarin diflomasiyya a yankin domin hana barkewar yaƙi. 
An tabbatar da zagaye na biyu na tattaunawar, sai dai har yanzu ba a sanar da ranar da za a gudanar da shi ba.

A cewar IRNA, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya kuma yi jerin kiran waya da takwarorinsa na Turkiyya da Masar da Saudiyya domin sanar da su sabbin abubuwan da suka faru game da tattaunawar da Amurka a Oman.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form