Majalisar Dattawan Najeriya ta nada mambobi 12 domin yin aiki tare da Majalisar Wakilai kan kudirin gyaran Dokar Zabe, wanda ya haifar da cece-kuce a baya-bayan nan.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da nadin mambobin kwamitin a ranar Talata yayin zaman gaggawa na majalisar.
Mambobin kwamitin sun hada da Sanata Simon Lalong a matsayin Shugaba, Sanata Orji Uzor Kalu, Sanata Tahir Monguno, Sanata Adamu Aliero, Sanata Abba Moro, Sanata Asuquo Ekpenyong, Sanata Aminu Iya Abbas, Sanata Tokunbo Abiru, Sanata Niyi Adegbonmire (SAN), Sanata Jibrin Isah, Sanata Ipalibo Banigo da Sanata Onyekachi Nwebonyi.
Akpabio ya ce bayan tuntuba da shugabannin majalisar, an kara adadin mambobin daga tara zuwa 12. Ya bukaci kwamitin da su dauki aikin a matsayin lamari na gaggawa, yana mai bayyana fatan cewa za su kammala aikinsu cikin ‘yan kwanaki ko mako guda domin bai wa Shugaban Kasa damar sanya hannu kan kudirin dokar kafin karshen watan Fabrairu.
Shugaban Majalisar Dattawan ya kara da cewa za a mika sakamakon aikin kwamitin cikin gaggawa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa kafin karshen Fabrairu, sannan ya buga guduma don kaddamar da kwamitin a hukumance.
A halin da ake ciki, zaman majalisar ya rikice bayan Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Sanata Tahir Monguno (APC, Borno ta Arewa), ya daga batun tsari yana neman soke amincewar da majalisar ta riga ta yi wa Sashe na 60(3) na kudirin.
Monguno ya jingina bukatarsa da Dokoki 1(b) da 52(6) na Dokokin Tsayuwar Majalisar Dattawa na 2023 (da aka yi wa gyara), kuma Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi ta Tsakiya) ya mara masa baya.
Sai dai matakin nan take ya haifar da tashin hankali a zauren majalisar, inda sanatoci da dama suka daga batutuwan tsari domin nuna adawa.
Rikicin ya kara kamari lokacin da Monguno ya karanta Sashe na 60(3) ba tare da kalmar “a ainihin lokaci (real time)” ba, inda ya maye gurbin kalmar “turawa (transmission)” da “canjawa (transfer)”.
Sanata Enyinnaya Abaribe (APGA, Abia ta Kudu) ya yi kakkausar adawa, yana ta daga batutuwan tsari yayin da hayaniya ta barke a zauren majalisar.
A cewar shafi na 45 na rahoton Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Zabe, Sashe na 60(3) na kudirin ya tanadi cewa jami’in da ke jagorantar zabe zai tura sakamakon kowace rumfar zabe ta hanyar lantarki zuwa tashar IREV a ainihin lokaci, bayan an sanya hannu da hatimi a takardar EC8A kamar yadda doka ta tanada, tare da sa hannun ‘yan takara ko wakilan jam’iyyun da ke wurin.
A kololuwar sabanin, Sanata Abaribe ya yi kiran Dokar 72 ta Dokokin Tsayuwar Majalisar, yana neman a kada kuri’a ta hanyar rarrabuwa (division).
Tags
Labarai
