Gwamnatin Pakistan ta bayyana cewa ba za ta shiga wata tattaunawa da Afghanistan ba, matuƙar hare-haren da ake kaiwa daga iyakar Afghanistan zuwa cikin Pakistan ba su tsaya ba.
A cewar jami’an Pakistan, tsaron ƙasar ya tabarbare sosai sakamakon hare-haren da ake zargin ƙungiyoyin mayaka na kaiwa daga cikin Afghanistan.
Pakistan ta ce tana zargin gwamnatin Taliban da gazawa wajen dakile ayyukan ƙungiyoyin da ke kai hari kan Pakistan.
Pakistan ta jaddada cewa ba za ta zauna a teburin tattaunawa ba har sai an ɗauki matakan gaggawa don dakatar da hare-haren da ake zargin ƙungiyar Tehrik-e-Taliban Pakistan ke kaiwa daga cikin Afghanistan. Gwamnatin ta ce kare rayuka da dukiyar ’yan ƙasarta ne babban abin da ya sa take ɗaukar matakan tsaro masu tsauri.
A martaninta, gwamnatin Taliban a Kabul ta musanta zargin ba da mafaka ga ’yan bindiga, tana mai cewa a shirye take ta shiga tattaunawa domin rage tashin hankali da dawo da zaman lafiya a iyakar ƙasashen biyu.
Rahotanni sun nuna cewa an samu musayar wuta da hare-hare a wasu yankunan iyaka, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da masu gudun hijira.
Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, ciki har da Majalisar Ɗinkin Duniya, sun yi kira ga bangarorin biyu da su rage zafi tare da komawa hanyar diflomasiyya domin kauce wa faɗa mai faɗi.
Masu sa ido na ganin wannan rikici na ɗaya daga cikin mafi muni tsakanin Pakistan da Afghanistan cikin ’yan shekarun nan, kuma yana barazana ga zaman lafiyar yankin gaba ɗaya.
News Translation in English Language.
Pakistan Says ‘No Dialogue’ with Afghanistan as Attacks Continue.
Islamabad/Kabul – The government of Pakistan has declared that it will not engage in dialogue with Afghanistan as long as attacks originating from Afghan territory continue.
Pakistani officials say the country’s security has sharply deteriorated due to assaults allegedly carried out by militant groups operating from within Afghanistan. Islamabad accuses the Taliban government of failing to prevent groups targeting Pakistan.
Pakistan emphasized that it will not sit at the negotiating table until urgent measures are taken to halt attacks by Tehrik-e-Taliban Pakistan from Afghan soil. The government stressed that protecting the lives and property of its citizens is its top priority.
In response, the Taliban authorities in Kabul denied providing sanctuary to militants and stated they are willing to enter talks to reduce tensions and restore peace along the border.
Reports indicate ongoing exchanges of fire and cross-border attacks, resulting in casualties and displacements. International organizations, including the United Nations, have called on both sides to de-escalate and return to diplomatic channels to avoid a wider conflict.
Observers say this marks one of the most serious escalations between Pakistan and Afghanistan in recent years, posing a significant threat to regional stability.
Tags
Labarai
