Iran ta tabbatar da harba da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙi zuwa Israi'la, a matsayin ramuwar gayya

Iran ta tabbatar da harba da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙi zuwa Israi'la, a matsayin ramuwar gayya

Rundunar Juyin juya halin Musulunci ta Iran ta tabbatar da harba da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙi zuwa Israi'la, a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai mata.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, IRGC ta ce harin da ta kai martani ne kai tsaye ga abin da ta bayyana a matsayin hare-haren hadin gwiwa na Amurka da Isra’ila da suka afkawa wasu wurare a Iran, ciki har da muhimman wuraren soja.

Rahotanni daga Isra’ila sun nuna cewa an ji ƙarar kararrawar gargaɗi a wasu sassan ƙasar, yayin da hukumomi suka umurci jama’a da su nemi mafaka domin kare rayukansu. 
Har yanzu dai ana tantance sakamakon harin, ciki har da ko an samu asarar rayuka ko barnar dukiya.

Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa wannan lamari na nuna babban ƙarin tsanani a rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila, wanda yanzu ya wuce matakin hare-haren wakilai zuwa fuskantar juna kai tsaye tsakanin manyan ƙasashen.

Al’ummar duniya na ci gaba da sa ido kan lamarin, yayin da ake fargabar cewa wannan rikici na iya janyo faɗaɗar yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya idan ba a samu gaggawar shiga tsakani ta diflomasiyya ba.

News Translation in English Language.

Iran Launches Missiles and Drones at Israel in Retaliation.

Iran’s Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) has confirmed launching missiles and unmanned combat drones at Israel in retaliation for attacks by the United States and Israel.

In a statement, the IRGC said the strikes were a direct response to what it described as coordinated US-Israeli attacks on Iranian targets, including key military sites.

Reports from Israel indicate that air-raid sirens were heard in several areas, with authorities instructing residents to seek shelter for their safety. The full impact of the strikes, including casualties or property damage, is still being assessed.

Security experts say the incident marks a significant escalation in the ongoing Iran-Israel conflict, which has now moved beyond proxy attacks to direct confrontation between the two states.

The international community is closely monitoring the situation, with fears that the conflict could escalate further in the Middle East if urgent diplomatic intervention is not undertaken.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form