Ƙasar Amurka Za Ta sake Aikewa da Ƙarin Sojoji Zuwa Najeriya.
Gwamnatin Amurka na shirin tura sojoji kimanin 200 zuwa Najeriya domin ƙara taimakawa a yaƙin da ƙasar ke yi da matsalar rashin tsaro, kamar yadda jaridar The New York Times ta ruwaito.
Wannan ƙarin runduna za ta haɗu da ƙananan rundunonin sojojin musamman na Amurka da ke Najeriya tun da farko, waɗanda ke taimaka wa jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan ta’adda da sauran masu tayar da kayar baya.
A makon da ya gabata ne dai, kwamandan United States Africa Command (AFRICOM), Janar Dagvin R. Anderson, ya tabbatar da cewa Amurka ta tura ƙungiyar ƙwararru zuwa Najeriya. Ya ce ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda suka tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro a yankin.
A cewar rahoton, sabbin sojojin Amurka ba za su shiga fagen yaƙi kai tsaye ba; aikin su shi ne horaswa da bayar da ƙwarewar fasaha ga sojojin Najeriya wajen yaƙi da ’yan bindiga da ’yan ta’adda. An ce za a tura su wurare daban-daban a faɗin ƙasar.
Amurka ta ƙara mayar da hankali kan Najeriya ne bayan Shugaba Donald Trump ya sake ayyana ƙasar a matsayin wacce take ba wasu bangaren Al'umma fifiko a ƙarshen shekarar da ta gabata, bisa zargin tsananta wa mabiya addinin Kirista.
Duk da haka, gwamnatin Najeriya ta musanta zarge-zargen, tare da aika tawaga mai ƙarfi ƙarƙashin jagorancin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, zuwa Amurka.
A watan Disamba, wata tawagar Amurka ƙarƙashin jagorancin ɗan Majalisa Riley Moore ta ziyarci Najeriya domin bincike kan zargin hare-haren da ake kai wa Kiristoci, inda suka gana da waɗanda matsalar tsaro ta shafa.
Rahoton ya nuna cewa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu ya ƙara ƙarfi, musamman bayan harin Kirsimeti da aka kai kan wuraren ISIS a Jihar Sokoto, wanda ya samu tallafin bayanan leƙen asiri daga jiragen sa-ido na Amurka da suka tashi daga Ghana.
Janar Dagvin R. Anderson ya sake ganawa da manyan jami’an Najeriya a wannan watan, yayin da mataimakinsa, Laftanar Janar John Brennan, ya kai ziyara Abuja a watan da ya gabata domin sanar da ƙarfafa dangantakar soji tsakanin Najeriya da Amurka.
Tags
Labarai
