Tinubu Ya Nada Ambasada Ismail Abba Yusuf a Matsayin Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON)
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Daraktan Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON).
Mai bai wa Shugaban kasa shawara na musamman kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya ce nadin yana karkashin amincewar Majalisar Dattawa, bisa tanadin sashe na 3(2) na Dokar NAHCON ta shekarar 2026.
A cewarsa, Shugaba Tinubu ya aike da wasika zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, inda ya bukaci a hanzarta tantancewa da tabbatar da nadin Ambasada Yusuf domin ya maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a wannan makon bayan shafe kusan watanni 14 a kan mukamin.
Sanarwar ta kara da cewa Ambasada Ismail Abba Yusuf gogaggen jami’in diflomasiyyar Najeriya ne, wanda ya taba rike mukamin Jakadan Najeriya na Musamman kuma Cikakken Wakili a Jamhuriyar Turkiyya daga shekarar 2021 zuwa 2024.
Nadin ya zo ne sa’o’i 48 bayan Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya ajiye mukaminsa a matsayin shugaban hukumar.
Tags
Labarai
