Jirgin sama na Arik Air, Boeing 737-7GL, ya yi saukar gaggawa a filin Jirgin Sama na Benin bayan da ya fuskanci matsalar injin yana tsakiyar tafiya.

Jirgin sama na Arik Air, Boeing 737-7GL, ya yi saukar gaggawa a filin Jirgin Sama na Benin bayan da ya fuskanci matsalar injin yana tsakiyar tafiya.

Jirgin sama na Arik Air, Boeing 737-7GL, ya yi saukar gaggawa a filin Jirgin Sama na Benin a ranar Laraba, 11 ga Fabrairu, bayan da ya fuskanci matsalar injin yana tsakiyar tafiya.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin yana kan hanyarsa ne daga Lagos zuwa Port Harcourt lokacin da aka lura da lalacewar É—aya daga cikin injinansa a sama. Matukan jirgin sun dauki matakin gaggawa ta hanyar karkatar da jirgin zuwa Benin domin tabbatar da lafiyar fasinjoji da ma’aikatan jirgin.

Jirgin ya sauka lafiya ba tare da asarar rai ko jikkata kowa ba. Dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin sun sauka lafiya, yayin da hukumomin tsaro da na sufurin jiragen sama suka dauki matakan da suka dace bayan saukar jirgin.

Ana sa ran hukumomin kula da hadurra da binciken jiragen sama za su gudanar da bincike domin gano musabbabin lalacewar injin da kuma hana sake faruwar irin wannan matsala a nan gaba.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form