An yankewa wani dan Najeriya hukuncin daurin rai da rai bayan ya kashe tsohuwar budurwarsa, dalibar likitanci ƙasar Burtaniya.

An yankewa wani dan Najeriya hukuncin daurin rai da rai bayan ya kashe tsohuwar budurwarsa, dalibar likitanci ƙasar Burtaniya.

An yankewa wani dan Najeriya hukuncin daurin rai da rai bayan ya kashe tsohuwar budurwarsa, dalibar likitanci ƙasar Burtaniya.

Wata kotu a kasar Birtaniya ta yankewa Adedapo Adegbola dan shekaru 40 hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da laifin kashe tsohuwar budurwarsa, ‘yar shekara 23 kuma dalibar jami’a, Steph Irons, a birnin Nottingham na kasar Ingila.

A cewar rahoton Irish a ranar Alhamis, Kotun Nottingham Crown ta yanke wa Adegbola hukunci ne bayan da ya amsa laifin kashe Irons a gidanta dake Mapperley a ranar 21 ga Oktoba, 2025, biyo bayan tabarbarewar dangantakarsu. 
Kotun ta ji cewa sun hadu ne a yayin da suke aiki tare kuma sun yi soyayya da juna kafin su rabu.

Masu gabatar da kara sun shaida wa kotun cewa Adegbola ya damu kwarai da Irons bayan rabuwar su, inda ya sayi wukake guda biyu sannan ya hau motar haya zuwa gidanta. 
Ya bi bayanta ne a lokacin da ta fito waje domin zubar da shara, inda ya shiga cikin gidan, ya yi ta caka mata wuka.

An samu Rahoton kisan ne lokacin da abokan aikin Irons suka sami saƙonni masu ban tsoro daga wayarta. 
Kafin daga baya ‘yan sanda su gano gawarta a falon gidan, inda aka tabbatar da mutuwar ta a wurin.

Bayan kisan, Adegbola ya gudu, inda ya watsar da tufafinsa masu dauke da jini da sauran abubuwan da yayi kisan da su a kan titunan Mapperley da Carlton. 
'Yan sandan Nottinghamshire sun ce ya guda ta hanyoyin Mansfield da Worksop da Sheffield, da Hull kafin daga bisani ya mika wuya. 

Alkalin kotun ya yankewa Adegbola hukuncin daurin rai da rai, tare da hukuncin daurin shekaru 25 mafi karanci a gidan yari.

Inspector Stuart Barson, babban mai binciken, ya bayyana Irons a matsayin "mace mai kirki kuma mai tausayi" wacce rayuwarta ta gajarta a cikin "yanayi mai ban tsoro." 

A cikin wata sanarwa, mahaifiyar Irons ta ce mutuwar diyarta ta sa dangin cikin rudani. Iyalin sun bayyana dalibin da aka kashe, wanda ya yi burin samun digirin digirgir a fannin ilimin likitanci, a matsayin mai kauna, mai kulawa, kuma mai cika alkawari.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form