Jihar Kebbi ta dauki nauyin dalibai marasa galihu 35 zuwa kasashen waje domin karatun likitanci.

Jihar Kebbi ta dauki nauyin dalibai marasa galihu 35 zuwa kasashen waje domin karatun likitanci.

Jihar Kebbi ta dauki nauyin dalibai marasa galihu 35 zuwa kasashen waje domin karatun likitanci.

Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Dr. Nasir Idris ya jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da daidaito a fannin ilimi, inda ya bayyana cewa ba za a sake daukar yaran da suka fito daga gidaje mara galihu a matsayin zabi na biyu a jihar ba.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi a wajen bikin bankwana da ‘yan asalin jihar Kebbi su 35 da aka dauki nauyin ba su cikakken tallafin karatun likitanci da ilimin hada magunguna a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Idris ya ce da gangan gwamnatinsa ta ba wa hazikan dalibai fifiko, inda ya ce shirye-shiryen bayar da tallafin karatu a kasashen waje sau da yawa ‘ya’yan iyalai masu hannu da shuni ne suka mamaye su.

“A matsayina na Æ™wararren malami, na fahimci cewa ’ya’yan talakawa galibi suna da hazaka na musamman.

Shi yasa muka dage akan cancanta, da'a, da sadaukarwa,” inji shi.

Ya shawarci daliban da su ci gaba da mai da hankali da ladabi tare da ba su tabbacin ci gaba da samun tallafi daga gwamnati tare da bayyana shirye-shiryen daukar nauyin sauran matasa marasa galihu don yin karatun tukin jiragen sama da injiniyoyin jirage a kasashen waje.

Tun da farko, kwamishinan ilimi mai zurfi, Alhaji Isah Abubakar Tunga, ya ce daliban sun kammala tantance su domin yin karatun likitanci da hada magunguna a babbar kwalejin kiwon lafiya da ke Addis Ababa.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form