An sako basaraken nan da 'yan bindiga suka sace a fadarshi a jihar Kwara bayan ya shafe kusan wata daya a hannun su.

An sako basaraken nan da 'yan bindiga suka sace a fadarshi a jihar Kwara bayan ya shafe kusan wata daya a hannun su.

Basaraken Oniwo na Afin, Oba Simeon Olanipekun, wanda wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, ya samu ‘yanci bayan da aka ce iyalansa sun biya karin kudin fansa N12m. 

An sako sarkin ne a daren Laraba, 4 ga Fabrairu, 2026 bayan ya kwashe kusan wata guda a tsare.

An ruwaito cewa an sace sarkin ne tare da dansa, Olaolu, wanda mamba ne na hukumar masu yi wa kasa hidima ta kasa, a yayin wani mummunan hari da aka kai a fadar sa a jajibirin sabuwar shekara. 

An saki Olaolu makonni biyu bayan biyan kudin fansa na farko na N20m.

Wata majiyar ‘yan uwa da ta yi magana bisa sharadin sakaya sunanta saboda tabarbarewar tsaro, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an dauki tsawon lokaci ana tattaunawa a kai har aka sako basaraken.

“Gaskiya ne an saki sarkin ne a daren Laraba bayan mun biya Naira miliyan 12 da kuma bankunan wutan lantarki guda biyu baya ga Naira miliyan 20 da aka biya a baya” inji majiyar.

“Sun ajiye shi ne a wani matsugunin makiyaya da ke kusa da Oreke a karamar hukumar Ifelodun, daga nan ne aka kai shi sansanin sojoji da ke Oreke, inda suka tuntube mu.”

Majiyar ta kara da cewa sarkin yana samun kulawar likitoci a wani asibiti da ba a bayyana ba bayan ya sha fama da rauni a jiki da kuma ruhi a lokacin da ake tsare da shi.

Majiyar ta kara da cewa "Yanzu yana cikin koshin lafiya.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da sakin sarkin amma ta musanta cewa ba ta san wani kudin fansa ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa an saki sarkin ne biyo bayan daukar tsaurara matakan tsaro na hadin gwiwa a yankin.

Ta kara da cewa "Kuna sane da cewa ayyukan tsaro na hadin gwiwa da suke ci gaba da yi a wannan fanni inda 'yan bindigar suke tserewa, ba mu da masaniyar wani biyan kudin fansa, CP Adekimi Ojo ya kasance yana nuna rashin jin dadinsa kan biyan kudin fansa, kuma a ko da yaushe yana shawartar dangin wanda abin ya shafa da su rika baiwa jami'an tsaro sahihan bayanai."

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form