Wasu fusatattun matasa sun kona wani mutum har lahira bayan an zarge shi da kashe yaro tare da cire masa idanuwa a jihar Nasarawa.


Wasu fusatattun matasa sun kona wani mutum har lahira bayan an zarge shi da kashe yaro tare da cire masa idanuwa a jihar Nasarawa.

Wasu fusatattun matasa sun kona wani mutum mai suna Samaila Zariya har lahira sakamakon wani mummunan kisan gilla da aka yi wa wani yaro a unguwar Tsohon Kasuwa da ke garin Keffi a Jihar Nasarawa.
 
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 5 ga Fabrairu, 2026 a Unguwar Tsohon Kasuwa da ke garin.
 
A cewar shaidun gani da ido, an ce wanda ake zargin ya kashe yaron ne tare da cire masa kwayan idonsa a wani lamari mai ban tsoro da ya tayar da hankalin al’umma.
 
Rahotanni sun ce bayan faruwan lamarin lamarin ne, wasu gungun jama’a suka cafke wanda ake zargin tare da banka masa wuta kafin jami’an tsaro su shiga tsakani, Inda nan take aka kone shi ya koma toka.
 
Lamarin dai ya jefa al’ummar yankin cikin alhini, inda mazauna yankin suka bayyana lamarin a matsayin na dabbanci da rashin Imani da kuma ban tausayi. 
 
Da yawan Al'ummar yankin sun yi kira da a inganta tsaro da kuma gaggauta yin adalci domin hana afkuwar irin wannan a nan gaba.
 
Har yanzu dai hukumomin kasar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, amma an ce ana ci gaba da kokarin dawo da kwanciyar hankali tare da gudanar da bincike kan al’amuran da ke tattare da kisan da akayi.
 
Shugabannin al’umma sun bukaci mazauna yankin da su kasance masu bin doka da oda tare da kaucewa daukar doka a hannunsu.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form