An saye dukkan tikitin wasannin Kofin Duniya na 2026 — inji Shugaban FIFA.
Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya bayyana haka ne, inda ya ce buƙatar tikiti ta kai wani matsayi na tarihi a gasar, saboda miliyoyin mutane sun nemi tikitin wasannin fiye da adadin kujerun da ake da su.
Infantino ya ce gasar Kofin Duniya na 2026, wadda za a gudanar a ƙasashen Amurka da Kanada da Mexico, za ta ƙunshi wasanni 104, kuma dukkan su sun samu cikakken sayarwa tun kafin fara gasar.
Duk da haka, shugaban FIFA ya bayyana cewa har yanzu ana iya samun ƙananan tikiti a matakin sayarwa na ƙarshe ko kuma ta hanyar tsarin sayarwa ta biyu (resale) da FIFA ta amince da shi.
Ya ƙara da cewa wannan babban sha’awa daga masoya ƙwallon ƙafa na nuna irin yadda Kofin Duniya na 2026 zai kasance babbar gasa mafi girma a tarihin FIFA.
An sayar da tikitin gasar na 2026 daga farashin $1,000 zuwa $7,000 kwatankwacin N 140,000 zuwa N9,800,000, bisa la'akari da wasannin da za'a kalla.
Tags
Labarai
_1.jpeg)