Shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ’yan ƙasar da su yafe masa idan har ya taɓa yi musu wani laifi, yayin da ake shiga watan azumin Ramadan.
Tinubu ya yi wannan roƙo ne a lokacin taron Tafsirin Ramadan da aka gudanar a Masallacin Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ya ce watan Ramadan lokaci ne na tuba da neman gafara da haɗin kai da nuna tausayi ga juna.
Shugaban ya bayyana cewa shugabanci ba ya rasa kuskure, don haka ya nemi ’yan Najeriya da su yi masa afuwa idan akwai abin da ya yi da ya ɓata musu rai.
Ya kuma ƙarfafa ’yan ƙasar da su yi addu’a domin zaman lafiya da haɗin kai da samun nasara wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da tattalin arziki da ƙasar ke ciki.
Tinubu ya jaddada cewa azumi ba wai kamewa daga abinci da abin sha kaɗai ba ne, har da gyaran hali da taimakon juna da kuma ƙoƙarin gina ƙasa mai cike da zaman lafiya da adalci.
Tags
Labarai
