Dan wasan Newcastle, Gordon ya Zura kwallaye hudu, a wasan da Kungiyar Newcastle din ta lallasa Qarabag da ci 6–1 a wasan Zakarun nahiyar turai.

Dan wasan Newcastle, Gordon ya Zura kwallaye hudu

Dan wasan Newcastle, Gordon ya Zura kwallaye hudu, a wasan da Kungiyar Newcastle din ta lallasa Qarabag da ci 6–1 a wasan Zakarun nahiyar turai.

Ƙungiyar Newcastle United ta samu babbar nasara a wasan cike gurbin matakin 'yan 16 na gasar zakarun nahiyar turai bayan ta lallasa Qarabag FK da ci 6–1 a wasan farko da aka buga a birnin Baku.

Tauraron wasan shi ne Anthony Gordon, wanda ya ci kwallaye hudu a rabin Lokaci na wasan, abin da ya ba Newcastle cikakken iko tun da wuri. 
Gordon ya fara zura kwallon farko da wuri a minti 3, sannan ya kara wasu kafin hutun rabin lokaci, ciki har da bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Sauran kwallayen Newcastle sun fito ne daga ‘yan wasanta da suka taimaka wajen kara tsawaita tazarar cin kwallaye, yayin da Qarabag ta samu kwallo guda ta rage radadin shan kashi.

Wannan sakamako ya sa Newcastle ta kara kusantar tsallakewa zuwa zagayen gaba na Gasar Zakarun Turai kafin wasan su na biyu da za a buga a Ingila, inda Qarabag ke fuskantar babban kalubale na sakamakon wasan.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form