Hukumomin tsaron ƙasar Mexico sun tabbatar da mutuwar shahararren shugaban ƙungiyar dillalan miyagun ƙwayoyi, Nemesio Rubén Oseguera Cervantes, wanda aka fi sani da “El Mencho.”
El Mencho shi ne shugaban ƙungiyar Jalisco New Generation Cartel (CJNG), wadda ake ɗauka a matsayin ɗaya daga cikin ƙungiyoyin laifi mafi ƙarfi da hatsari a Mexico.
Rahotanni sun ce an kashe shi ne a yayin wani gagarumin farmaki da sojojin Mexico suka kai a jihar Jalisco, tare da haɗin gwiwar rundunar tsaron ƙasar da sauran hukumomin tsaro.
Bayan tabbatar da mutuwarsa, an samu tashin hankali a wasu sassan jihar Jalisco da kewaye, inda ake ganin an toshe manyan hanyoyi, an kona motoci, tare da musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar CJNG ne.
Hukumomi sun ce a yayin aikin, an kama wasu mutane da ake zargi da hannu a ayyukan laifi, tare da kwace makamai da kayan yaƙi. Gwamnatin Mexico ta bayyana cewa wannan nasara babbar nasara ce a yaƙin da ake yi da manyan ƙungiyoyin dillalan miyagun ƙwayoyi.
El Mencho ya shahara a duniya sakamakon jagorancinsa na CJNG, wadda ke da hannu wajen safarar miyagun ƙwayoyi da fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran laifuka masu tsanani.
Haka kuma, hukumomin Amurka sun daɗe suna nemansa tare da sanya ladan miliyoyin daloli kan duk wanda zai taimaka wajen kama shi.
Masu sharhi kan harkokin tsaro sun yi gargadin cewa duk da mutuwarsa, akwai yiwuwar rikice-rikice su ƙaru yayin da wasu ƙungiyoyi ko ragowar CJNG ke ƙoƙarin karɓar ragamar iko. Gwamnatin Mexico ta ce za ta ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
News Translation in English Language.
Mexican Drug Cartel Leader “El Mencho” Killed in Major Security Operation.
Mexico City – Mexican security authorities have confirmed the death of notorious drug cartel leader Nemesio Rubén Oseguera Cervantes, widely known as “El Mencho,” following a large-scale military operation in western Mexico.
El Mencho was the head of the Jalisco New Generation Cartel (CJNG), regarded as one of the country’s most powerful and violent criminal organizations. According to official reports, he was killed during a coordinated operation carried out by the Mexican Army with support from the National Guard and other security agencies in Jalisco State.
Following confirmation of his death, outbreaks of violence were reported in parts of Jalisco and nearby areas. These incidents included road blockades, burning vehicles, and armed confrontations, believed to be reactions by suspected cartel members.
Authorities said several suspects were arrested during the operation, while weapons, ammunition, and tactical equipment were seized. The Mexican government described the operation as a significant achievement in its ongoing fight against organized crime.
El Mencho was internationally known for leading the CJNG, a cartel linked to large-scale drug trafficking, extortion, kidnappings, and other serious crimes. He had long been one of the most wanted criminals by both Mexican and United States authorities, with a multi-million-dollar reward placed on his capture.
Security analysts have warned that despite his death, tensions may persist as rival factions or remaining CJNG elements attempt to assert control. The government has assured the public that security forces will remain on high alert to prevent further unrest and protect civilians.
Tags
Labarai
