A ranar Talata ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, Sani Malumfashi da wasu mutane biyu a gidan yari bisa zargin almundahanar Naira biliyan 1.
Alkalin kotun, James Omotosho, ya bayar da umarnin ne bayan da Malumfashi da wadanda ake zargin suka ki amsa laifuka shida a lokacin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC ta gurfanar da su gaban kuliya.
Mista Omotosho ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake tuhumar a gidan yari da ke Kuje, Abuja, har zuwa lokacin da za a saurari bukatar neman belinsu.

0 Comments:
Post a Comment