An daure uwargidan tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Kim Keon Hee na tsawon watanni 20 a gidan yari.
Kotu ta yankewa Kim Keon Hee, matar tsohon shugaban kasar Koriya ta kudu, Yoon Suk Yeol hukuncin zaman gidan yari na shekara daya da watanni takwas a yau Laraba saboda karbar cin hanci a lokacin da mijinta ke karagar mulki daga shekaran 2022 zuwa 2025, a daya daga cikin laifuka uku da take fuskanta.
Sai dai Alkalin ya baiyana cewa duka masu gabatar da kara da tawagar Kim Keon Hee na iya daukaka kara kan hukuncin.
Kotun ta samu Kim da laifin karbar cin hanci daga Cocin Unification Church mai cike da cece-kuce, da suka hada da jakar Chanel da abun wuyan lu'u-lu'u na Graff.
Amma ba ta same ta da laifin karkatar da hannun jari da hada baki tare da mijinta don samun kuri'un jin ra'ayin jama'a kyauta ba, saboda rashin isassun shaidu da ka'idojin iyakancewa - sannan kuma ta wanke ta saboda rashin karbar cin hancin jakar chanel Karo na biyu.
Masu gabatar da kara sun kiyasta cewa darajan hannun jari da cin hanci domin zaben jin ra'ayin Al'umma sun kai dalar Amurka 813,000.

0 Comments:
Post a Comment