Ƙasar Faransa ta ce tana goyon bayan yunkurin Tarayyar Turai na ayyana kungiyar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) a matsayin "kungiyar ta'addanci", tare da sauya adawa da matakin da a baya.
A cikin wata sanarwa da aka watsa ta kafar sada zumunta a ranar Laraba, ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya bayyana cewa Faransa ta yi Allah-wadai da matakin hukumomin Iran da suka dauka a baya-bayan nan kan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a fadin kasar.
"Tare da takwarorinmu na Turai, za mu dauki mataki gobe a Brussels a kan wadanda ke da alhakin wannan ta'asa, za a dakatar da su daga yankunan Turai kuma za a kulle kadarorinsu," in ji shi.
Ana sa rai "Faransa za ta goyi bayan sanya kungiyar kare juyin juya halin Musulunci a cikin jerin kungiyoyin ta'addanci na Turai a Lokacin taron."

0 Comments:
Post a Comment