Majalisar koli ta shari’a a Najeriya (SCSN) ta bukaci a tsige Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC daga mukaminsa Saboda zargin nuna kabilanci.
Majalisar koli ta shari’a a Najeriya (SCSN) a ranar Laraba ta bayyana cewa al’ummar musulmi ba za su amince da duk wani zabe da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar a karkashin jagorancin shugabanta Farfesa Joash Amupitan.
A jawabin da majalisar ta yi a yayin taron shekara-shekara da majalisar ta yi kafin watan Ramadan da kuma babban taronta a Abuja, majalisar ta yi kira da a tsige Amupitan, saboda rashin kwarin gwiwa kan amincinsa na yin adalci ga dukkan addinai a Najeriya.
Shugaban Majalisar, Sheikh Bashir Aliyu Umar, ya ce wannan rashin yarda ya samo asali ne bayan da Amupitan ya rubuta takaitaccen bayani yana mai cewa Kiristoci a Najeriya suna fama da kisan kare dangi—da’awar da gwamnatin tarayya ta sha yin watsi da ita.
Haka zalika a baya Amupitan ya bayyana tada kayar bayan Boko Haram da hare-haren "Fulani makiyaya" a matsayin wani shiri na yaki da kiristoci da ke bukatar shiga tsakani na kasa da kasa.
An bayyana shi a matsayin wanda ya bayar da gudummawa wajen wallafa littafi mai suna kisan mummuke a Najeriya da Tasirin Al'ummar Duniya na 2020, wanda Kwamitin Kasa da Kasa kan Najeriya (ICON) da Kungiyar Gina Zaman Lafiya da Adalci (PSJ) suka fitar.
Rahoton ya tattara zargin kashe kiristoci da ake yi a Najeriya tare da yin kira da a dauki mataki a duniya. Amupitan ya rubuta wani babi mai shafuka 80 mai suna Legal Brief: Kisan Kiyashi a Najeriya, wanda ya yi nuni da cewa girma da tsarin kashe-kashe da tarwatsa Kiristoci sun kai matsayin kisan kiyashi a karkashin dokokin kasa da kasa.
A cikin Takaitaccen bayanin nasa ya kuma zargi gwamnatin tarayya da gazawa wajen kare al’ummomin da abin ya shafa da kuma tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.

0 Comments:
Post a Comment