Tinubu ya aika da jakadu hudu zuwa Faransa da Amurka da Birtaniya da Turkiyya.
Shugaba Bola Tinubu ya amince da nada jakadu hudu da aka nada a kasashen Faransa da Amurka da Birtaniya da kuma Turkiyya.
An sanar da amincewar ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar a yau Alhamis.
"Shugaban kasa ya amince da nada jakadu hudu daga cikin 68 da majalisar dattawa ta tabbatar a watan Disambar da ya gabata," in ji Onanuga.
Sanarwar ta hada da Ambasada Ayodele Oke da Kanar Lateef Are da Ambasada Amin Dalhatu da tsohon gwamnan jihar Kebbi, Usman Isa Dakingari Suleiman, wadanda zasu yi aiki a Kasashen Faransa da Amurka da Ingila da Turkiyya.

0 Comments:
Post a Comment