Donald Trump yace Amurka ta aika da Jirgin ruwan Armada zuwa tekun fasha domin sa ido akan Iran

Donald Trump yace Amurka ta aika da Jirgin ruwan Armada zuwa tekun fasha domin sa ido akan Iran

Donald Trump yace Amurka ta aika da jirgin ruwan 'Armada' dake dakon jiragen yaki zuwa yankin tekun fasha domin duba yiwuwar kaima Iran hari.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Jirgin ruwan "armada" na sojojin ruwan Amurka na kan hanyarsa ta zuwa yankin tekun Fasha, inda aka fi mai da hankali akan Iran, yayin da jami'ai suka ce ana sa ran sauran jiragen dakon kayan yaki za su isa yankin Gabas ta Tsakiya a cikin kwanaki masu zuwa.

Trump ya fadawa manema labarai a tashar jirgin saman Air Force One jiya Alhamis yayin da yake dawowa daga taron tattalin arzikin duniya a Davos, Switzerland, cewa Trump"Muna kallon Iran,".

"Muna da babban karfi da ke zuwa Iran,"
"Na gwammace kada in ga wani abu ya faru, amma muna kallon su sosai," in ji shi.

"Kuma watakila ba za mu yi amfani da shi ba ... muna da jiragen ruwa da yawa da ke zuwa wannan yankin, muna da babban flotilla da ke tafiya a wannan hanyar zuwa yankin, kuma za mu ga abin da zai faru," in ji shi.

Sanarwar da Trump ya bayar game da tura sojojin ruwan Amurka na zuwa ne bayan da ya bayyana a makon da ya gabata kan barazanar daukar matakin soji akan Iran, bayan da ya ce, yana samun tabbacin cewa Tehran ba za ta zartar da hukuncin kisa kan masu zanga-zangar tsadar rayuwa a ƙasar ba.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: