Hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi da masu gudanar da yawon bude ido sun yi kira ga ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya da ta ƙara guraben aikin Hajji daga 50,000 aka ware wa Najeriya zuwa 66,910 domin gudanar da aikin Hajjin 2026.
Sun bukaci a maido da adadin guraben aikin Hajjin 66,910 wanda da aka ware wa Najeriya a shekaran 2025 domin a samu karin yawan maniyyata a wannan shekara.
Masu ruwa da tsakin sun mika wannan bukata ne a jiya Alhamis yayin da suke ganawa da tawagar kasar Saudiyyan karkashin jagorancin Farfesa Ghassan Al-Nuaimi.
An gudanar da taron ne gabanin ziyarar aiki da mai girma ministan Hajji da Umrah, Dr Tawfiq bin Fawzan Al-Rabbiah, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 3 ga watan Fabrairu.
Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Yobe, Alhaji Aliyu Usman, ya koka kan yadda rage guraben aikin Hajji zai hana ‘yan Najeriya da dama damar zuwa aikin hajji.
Manajan Darakta/Shugaba Ar-rahama na aikin Hajji da Umrah, Ustaz Khidir Usaefat, ya kuma bayyana rashin isassun kason aikin Hajji da aka ware wa maniyyatan Najeriya don gudanar da aikin Hajjin 2026.

0 Comments:
Post a Comment