An sako amarya da kawayenta da sauran 'yan biki bayan kwashe kwanaki 49 a hannun ‘yan bindiga a jihar Sokoto.
Zaman jimami ya kare a kauyen Chacho da ke karamar hukumar Wurno a jihar Sokoto, inda da aka sako wata Amarya tare da kawayenta bayan sun kwashe kusan kwanaki 49 a hannun masu garkuwa da mutane.
Majiyoyin cikin gida sun tabbatar da cewa an sako wadanda lamarin ya rutsa da su ne bayan da iyalansu suka tara kudin fansa naira miliyan 10, tare da sabbin babura guda uku da sauran kayayyaki, lamarin da ya nuna yadda rashin tsaro ya yi kamari a yankunan karkara.

0 Comments:
Post a Comment