Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya raba dubunnan mutane da muhallinsu a ƙasar Mozambique.
Mummunan ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama ya haddasa ya tilastawa dubban mutane tserewa daga gidajensu a ƙasar Mozambique, inda da yawa daga cikin mazauna kasar suka makale a saman rufin gidajensu Sakamakon ambaliyan, kamar yadda kungiyoyin agaji da shaidu gani da ido suka bayyana.
Fiye da mutane 620,000 ne bala'in ambaliyar ruwan ya shafa, wanda ya lalata gidaje sama da 72,000 tare da lalata muhimman ababen more rayuwa da suka hada da tituna, gadoji, da wuraren kiwon lafiya, kamad yadda kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent (IFRC), wacce ke ba da agajin gaggawa ta sanar.

0 Comments:
Post a Comment