Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai a kudancin Lebanon Inda mutum 2 suka mutu tare da jikkata 20 duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Isra'ila ta sanar da kai hari kan mashiga guda hudu da ke kan iyakar Syria da Lebanon, wanda ta ce Kungiyar Hizbullah ce ke amfani da su wajen safarar makamai, biyo bayan harin da aka kai a kudancin kasar Lebanon a jiya laraba wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla biyu tare da jikkata kusan 20.
Harin na baya bayan nan da Isra'ila takai ya zo ne duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka ta Jagoranta, wanda ya kawo karshen yakin da aka shafe sama da shekara guda ana gwabzawa tsakanin Isra'ila da mayakan Hizbullah a kasar Labanon a shekara ta 2024.
_2.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment