Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da samar da cikakken tallafin jin kai ga Haruna Bashir, wanda aka kashe ‘ya’yansa shida da matarsa a unguwar Chiranci Dorayi da ke jihar.
Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar bayan ziyarar ta'aziyya da ya kai ga iyalan.
An kashe Fatima Abubakar mai shekaru 35 da ‘ya’yanta shida a gidansu ranar Asabar.
Bayan bincike rundunar ‘yan sandan jihar ta samu nasaran kama mutane uku da suka hada da Umar Auwalu mai shekaru 23, dan uwa ga matar da ta rasu, wanda ya amsa laifin kai harin.
Bature, a cikin sanarwar, ya ce kunshin tallafin da Gwamnan ya bashi ya hada, da daukar nauyin aikin Hajji da Umrah, samar da sabon gida da cikakken tallafin gwamnati don taimaka mashi wajen sake gina rayuwarsa.

0 Comments:
Post a Comment