Sunday Igboho ya yabawa Tinubu da sarakunan gargajiya game da rawan da suka taka wajen dawowarsa daga gudun hijira.

Sunday Igboho ya yabawa Tinubu da sarakunan gargajiya game da rawan da suka taka wajen dawowarsa daga gudun hijira.

Dan rajin kare hakkin kabilar Yarabawa, Sunday Igboho ya yabawa Tinubu da sarakunan gargajiya game da rawan da suka taka wajen dawowarsa daga gudun hijira.

Dan rajin kare hakkin kabilar Yarabawa, Cif Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnonin Kudu maso Yamma da kuma sarakunan gargajiya a kasar Yarbawa bisa ‘yancin da ya samu tare da komawa Najeriya bayan ya kwashe kusan shekaru biyar yana gudun hijira a ƙasar Jumhuriyar Benin.

Igboho ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Dan gwagwarmayar ya dawo kasar ne a ranar Litinin bayan ya gudu daga Najeriya a shekarar 2021, lokacin da gwamnatin marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana nemansa bisa zargin tara makamai da alburusai.

A ranar 1 ga Yuli, 2021, jami’an ma’aikatar harkokin wajen kasar, tare da jami’an soji, sun kai samame a gidansa da ke Ibadan a kokarin kama shi. 
A yayin farmakin dai an kashe mataimakansa biyu, yayin da aka kama wasu 13.
Tun daga wancan Lokacin yake gudun hijira a makwabciyar Najeriya, Jumhuriyar Benin.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: