Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya koma makaranta a matsayin dalibin shari'a a jami'ar Arewa maso Yamma dake Kano.
Sarkin Sanusi ya fara karatun ne a Jami’ar Arewa maso Yamma, (North-West University) da ke Kano, bayan ya shiga aji 200 a fannin shari’a.
Hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna sarkin a cikin aji a ranar Talata, 20 ga Janairu, tare da sauran daliban da suke karatun digiri a fannin shari'a.
Jami'ar ta baiwa Sanusi gurbin Karatun digiri na musamman ne a fannin shari'a wato Bachelor of Law a turance.
A cewar Jami'ar, an ba da wannan damar ne saboda irin dimbin gogewar da yake da ita a harkar mulki da tattalin arziki da kuma aikin gwamnati.
Sarki Sanusi, wanda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya riga ya kammala digirin digirgir (Phd) dinsa a shekaran da ta gabata a Jami'ar Landan (University of London) dake ingila.

0 Comments:
Post a Comment