Dan ƙunar ɓaƙin wake ya kai hari Kan ayarin motocin Sojin Najeriya a jihar Borno inda ya kashe sojoji 5.
Wani dan kunar bakin wake ya abka cikin jerin gwanon motocin sojoji a Timbuktu triangle a jihar Borno, inda ya kashe sojoji 5 tare da jikkata wasu dakaru da ba a tantance adadinsu ba.
Rahotannin na cewa harin ya rutsa da manyan jami’an soji biyu – Manjo da Laftana daya.
"Haka zalika harin ya haifar da babbar illa ga kayan aikin sojojin wadanda aka yi amfani da su wajen kai hare-hare akan 'yan ta'adda a makon da ya gabata.
Rahotan ya kara da cewa 'yan ta’addan sun yi amfani da wata mota makare da bama-bamai ne wajen kutsawa cikin ayarin sojojin.
Sojojin na dawowa ne daga wani samame da suka yi nasarar fatattakar wasu sansanonin Kungiyar masu tayar da kayar baya tare da kashe da dama daga cikinsu a lokacin da aka ce harin ya afku.

0 Comments:
Post a Comment