Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya amince da gayyatar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi masa na shiga cikin "kwamitin zaman lafiya" na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.
Ofishin shugaban na Isra'ila ne ya sanar a shafinsa na sada zumunta a jiya Laraba, Inda yace, Netanyahu zai shiga wannan kwamiti, duk kuwa da cewa an kaddamar da shine a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Kungiyar Hamas kashi na biyu na kawo karshen yakin kisan kare dangi da Isra'ila ke yi a Gaza.
Trump ya gayyaci shugabannin duniya da dama don shiga kwamitin, wanda ya yi hasashen zai sa ido wajen "sake gina zirin Gaza da mayar da hankalin wajen saka hannun jari a yankin.
Sai dai Koyaya, shigar Netanyahu zai ƙara damuwa game da haƙiƙanin wannan kwamitin, wanda Trump zai jagoranta?

0 Comments:
Post a Comment