Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da sace mutane jihar Kaduna.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da sace mutane jihar Kaduna.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun sace mutanen da dama a karamar Hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, bayan ta musunta hakan da farko.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta sanar da cewa wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da mutane da dama a karshen mako, bayan Hukumar ta musanta faruwan lamarin a baya.

A wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Talata, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Benjamin Hundeyin, ya ce hakika an yi garkuwa da mutane a karamar Hukumar Kajuru ta jihar Kaduna a ranar Lahadi, kuma ‘yan sanda sun kaddamar da ayyukan tsaro “tare da mayar da hankali sosai wajen ganowa da ceto wadanda lamarin ya shafa da kuma dawo da kwanciyar hankali a yankin.

Hundeyin ya ce musanta faruwan lamarin da farko da jami’ai suka yi na “da nufin hana fargabar da kokarin tabbatar da gaskiyan lamarin”. 
Sai dai Sanarwar ‘yan sandan ba ta bayyana adadin mutanen da aka sace ba.

A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Associated Press, dan majalisar dokokin jihar Kaduna, Usman Danlami Stingo ya ce adadin mutanen da aka sace ya kai 168.

Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya reshen arewacin kasar, Reverend John Hayab, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho a ranar Litinin cewa, an yi garkuwa da akalla masu ibada Kiristoci 172, sannan tara daga baya suka tsere, inda 163 suke hannun yan ta'addan.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: