Kungiyar kwallon kafar Bodoe/Glimt ta lallasa Manchester City da ci 3-1 a wasan rukuni da cin kofin zakarun nahiyar tura, UEFA Champions league.
Dan wasan gaban Bodoe/Glimt, Kasper Høgh ne ya fara zura kwallon farko a ragar City a minti na 22 da fara wasan kafin daga bisani ya zura ta biyu a minti na 24.
Bayan an dawo hutun rabin Lokaci ne sai Bodoe/Glimt ta Kara zura kwallo ta uku a ragar City ta hannun Jens Hauge a minti na 58, kafin Rayan Cherki ya farke wa City din kwallo daya a minti na 60.
Nasaran da Bodoe/Glimt din ta samu ya sake bata karfin gwiwar ganin ta kare a cikin Kungiyoyi 24 domin samun daman buga matakin 'yan 16 na gasar, Inda ta koma mataki na 27 da maki 6.
Sai Manchester City wacce ta koma matakin na 6 da maki 13.
%20(6)_3.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment