Ƙasar Guatemala na zaman makokin ‘yan sanda 10 da ‘yan daba suka kashe a lokacin tarzoman gidan yari da ta barke a ƙasar.
An kashe jami’an ‘yan sanda 10 a wani harin gungun ‘yan bindiga da suka hada kai a kasar Guatemala wanda ya fara da tarzomar a wasu gidajen yari uku a ƙasar, Inda daga bisani tarzoman ta fantsama kan titunan babban birnin kasar domin ramuwar gayya, lamarin da ya sa gwamnatin ƙasar kafa dokar ta-baci.
Gwamnatin ƙasar ta tabbatar da cewa 'yan sanda 10 ne suka mutu bayan hare-haren, yayin da 'yan majalisar dokokin kasar suka amince da dokar ta-baci ta kwanaki 30, wacce ta fara aiki a ranar litini bayan sun kada kuri'ar amincewa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

0 Comments:
Post a Comment