Wata babbar mota kirar kanta ta afkawa dandazon jama'a a gefen hanya, inda tayi sanadin mutuwar mutum uku, tare da jikkata 40 a jihar Yobe.
An tabbatar da mutuwar mutane uku, yayin da wasu kimanin 40 suka samu raunuka bayan da wata babbar mota kirar kanta ta afkawa mutanen da ke zaune a bakin titi a hanyar Gombe zuwa Potiskum a jihar Yobe.
Hadarin ya afku ne da misalin karfe 2:30 na ranar yau Laraba a kusa da garin Badejo da ke karamar hukumar Potiskum.
Shaidun gani da ido sun ce da alama motar tana gudun wuce da ya wuce kima kafin daga bisani ta afka wa wadanda ke gefen hanyar.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya Paul Andrew, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin.

0 Comments:
Post a Comment