An yankewa dan bindigan da ya kashe tsohon Firaminastan Japan, Shinzo Abe hukuncin daurin rai da rai.
An samu dan bindigan da ake zargi da kashe tsohon Firaministan Japan, Shinzo Abe da laifin kisan gilla, inda aka yanke mashi Hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.
An yanke Hukuncin ne bayan shafe fiye da shekaru uku da kisan gillar da aka yi wa Shinzo Abe wanda yaja hankalin duniya.
Harbin ya kasance abun mamaki a kasar da ba ta da yawan samun tashin hankalu masu alaka da harbin bindiga, Wanda hakan ya haifar da bincike kan alakar da ake zargi tsakanin fitattun 'yan majalisun dokokin kasar masu ra'ayin mazan jiya da wata kungiya ta asiri mai suna "Unification Church".

0 Comments:
Post a Comment