Kungiyar CAN ta Arewa ta yi watsi da kiran da aka yi na a tsige Shugaban INEC, ta kuma yi gargadin a guji siyasantar da addini

Kungiyar CAN ta Arewa ta yi watsi da kiran da aka yi na a tsige Shugaban INEC, ta kuma yi gargadin a guji siyasantar da addini

Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN a jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin tarayya Abuja, sun yi watsi da kiran da Majalisar Koli ta Shari’ah a Najeriya (SCSN) ta yi na a tsige Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, inda ta bayyana bukatar a matsayin wani yunkuri na siyasantar da addini da kuma lalata wata babbar cibiyar kasa.

Tun da farko dai Majalisar Shari’ar Musulunci ta yi kira da a gaggauta tsige Shugaban Hukumar ta INEC, saboda nuna damuwarsa a wani takaitaccen bayani yayi, inda rahotanni suka ce ya amince da ikirarin da ake yi na cin zarafin Kiristoci a Najeriya wanda Gwamnatin ƙasar Tasha musantawa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta CAN ta Arewa, Rev. Joseph John Hayab da babban sakatarenta, Bishop Mohammed Naga, kungiyar ta kiristocin ta bayyana dalilin da ya sa suka gabatar da wannan bukata, inda ta tambayi ko wanene ke daukar nauyin wannan kiran da kuma dalilin da ya sa ake samun irin wadannan muradu a karkashin wata kungiya ta addini.

Kungiyar CAN ta Arewa ta yi gargadin cewa yin amfani da addini a matsayin madogara wajen kokwanton mutuncin masu rike da mukaman gwamnati abu ne mai hadari kuma yana iya ruruta wutar rikicin addini.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: