Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai munanan hare-hare wanda ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas a watan Oktoban 2023, inda aka kashe Falasdinawa mutum hudu a yankin al-Sanafour na birnin Gaza da yaki ya daidaita.
Haka zalika Isra'ila ta yi nuni da cewa za ta bayar da damar adadin mutanen da za su tsallaka mashigin Rafah zuwa Masar, sai dai ba ta ambaci adadin kayan agajin da zata bayar da damar shiga da shi zirin na Gaza ba kamar yadda kasashen duniya suka bukata ba.
Yaƙin kisan ƙare dangi da Isra'ila ke yi a Gaza ya kashe akalla mutane 71,660 tare da raunata 171,419 tun da aka fara shi a watan Oktoban 2023.
Kimanin mutane 1,139 aka kashe a Isra'ila yayin harin da Hamas ta jagoranta a ranar 7 ga Oktoba, 2023, inda aka kama kusan 250 a wancan Lokacin.
_1.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment