Kasar Cuba ta karrama sojojinta 32 da aka kashe a harin da Amurka ta kai kan kasar Venezuela a farkon watan nan wanda yakai ga sace shugaban Kasar Venezuela, Nicolas Maduro.
Gawarwakin sojojin kasar ta Cuba da hukumomin leken asiri, sun isa filin jirgin saman kasar ta Cuba dake babban birnin ƙasar, Havana, a cikin akwatunan gawa da aka lullube da tutar kasar ta Cuba a safiyar ranar Alhamis.
Shugaban Cuba, Miguel Diaz-Canel da Raul Castro, tsohon shugaban kasar mai shekaru 94, sun hallara cikin cikakken kakin soja don karbar gawarwakin.
Diaz-Canel ya yaba wa sojojin a farkon wannan makon, yana mai cewa "sun fada cikin jarumtaka domin kare 'yancin kan wata kasa 'yar uwa".
A wajen taron na ranar Alhamis, ministan harkokin cikin gida Janar Lazaro Alberto Alvarez ya kuma nuna jin dadin kasar ga sojojin da ya ce sun yi yaki da harsashi na karshe a harin da sojojin Amurka suka kai a Caracas babban birnin kasar Venezuela a ranar 3 ga watan Janairu.

0 Comments:
Post a Comment